Mai daukowa gwamnan Kano rahoto a hukumar kula tarihi da al’adu Sadiq Gentle ya rasu, kwanaki kadan bayan wasu ƴan daba sun kai masa mummunan hari cikin dare.
Rahotanni sun bayyana cewa harin da aka kai masa ya jefa shi cikin mawuyacin hali, inda aka garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa.
Sai dai, duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi, ya rasu sakamakon munin raunukan da ya samu.