Wani jirgi mai saukar ungulu da ke ɗauke da matuƙansa uku da fasinjoji biyar ya yi hatsari a yankin Ashanti na ƙasar Ghana da safiyar Laraba.
Jirgin dai ya yi hatsarin ne bayan ya gaza tuntuɓar cibiyar da ke bibiyar jirgin.
Hotuna da ake kyautata zaton na jirgin ne da ya kwalmaɗe suna ta yawo a soshiyal midiya.
Akwai rahotanni da ke nuna cewa akwai jami’an gwamnati da ke cikin jirgin.
Ana sa ran fadar shugaban ƙasar ta Ghana za ta yi wa ƴan jarida bayani dangane da abin da ke faruwa.