Nafisa Abdullah Aminu, ɗaliba mai shekaru 17 daga Jihar Yobe a Arewa maso Gabashin Najeriya, ta samu nasarar lashe matsayi na farko a gasar ƙasa da ƙasa ta iya Turancin Ingilishi TeenEagle Global Finals 2025 — da aka gudanar a birnin London, babban birnin Ingila.
Nafisa ta doke sama da ɗalibai 20,000 da suka fito daga ƙasashe 69 na duniya domin samun wannan gagarumar nasara, lamarin da ya janyo mata yabo daga sassa daban-daban na ƙasa da ƙetare.