Rahotanni daga jihar Zamfara sun nuna cewa ƴanbindiga sun yi garkuwa da mutum 60 a ƙauyen Sabon Garin Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura a ƙarshen mako.
dai sun nuna cewa ƴanbindigar ɗauke da muggan makamai haye a kan babura sun yi wa ƙauyen ne shigar ba-zata ranar Asabar, in ji Isa Sani wani mazaunin ƙauyen da ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
“Da shigarsu ƙauyen ba su wata-wata ba sai suka fara da harbin kan mai-uwa-da-wabi inda kuma daga bisani suka yi garkuwa da mutum 60 da suka haɗa da ƙananan yara da ƴanmata. Kawo yanzu ba mu ji komai daga gare su ba. Ko’ina ya yi tsit.” In ji Isa.
Ƴanbindigar sun kuma kashe wani manomi sannan sun yi awon gaba ɗansa a wani ƙauye da ke maƙwabtaka mai suna Rogoji.