Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) ta gargadi mutane kan yin taka tsantan da jabun takardar naira 1,000 dake yawo a jihar Kwara.
Shugaban Hukumar Abdulganiyu Dare ya sanar da a garin Ilorin.
Dare ya ce Hukumar ta yi wannan gargaddin ne domin tabbatar da mutane da ‘yan kasuwa sun zama a fadake domin kare kansu da sanar’ar su daga karbar wadannan kudade.
Ya ce hukumar ta gano hakan ne a dalilin bayanan sirri da ta samu na yadda wasu suke kokarin kareda jihar da jabun takardar naira 1,000 masu lanba 364232 da 898248.
Ya ce alamun jabun kudin sun hada da dushewar hotunan dake kan kudin da wasu bangarorin kudin da basu yi dai-dai da wanda ake amfani da suka kasar nan ba.
Hukumar na kira ga mutane musamman masu harka da manyan kudade da kula domin guje wa karban jabun kudin.
“Mutanen dake kokarin yadda jabun kudin kan bada jabun kudade wa masu sana’ar kudi na POS domin saka musu kudaden a cikin asusun su ns banki.
“Hukumar za ta ci gaba da kokarin wayar da kan mutane kan jabun kudade da yadda za su iya gane su.
Dare ya ce hukumar za ya hada hannu da jami’an tsaro domin tabbatar da sun kamo duk wadanda ke da alaka da baza jabun kudade domin ganin an hukunta wu.