Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna goyon bayansa wajen sabon tsarin samar da cigaba a matakin mazaɓu da nufin bunƙasa cigaba daga tushe da tsamo miliyoyin mutane daga talauci a Najeriya.
Wannan shiri an kira shi ne da sabunta fatan ta hanyar samar da cigaba a matakin mazaɓu (RHWDP), wanda aka amince da shi a ranar Alhamis a yayin zama majalisar zartarwa (NEC) karo na 150 a fadar gwamnati da ke Abuja.
Shirin RHWDP zai shafi mazaɓu 8,809 a fadin jihohi 36 a matsayin wata hanya ta rage wa al’umma talauci kai tsaye da samar da wadataccen abinci da samar da wutar lantarki da inganta ayyukan more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki.
Wannan wani babban aiki ne na faɗaɗa shirin sabunta fata na shugaba Tinubu wanda ke fatan bunƙasa tattalin arziƙi ta hanyar samar Dala tiriliyan nan da 2030.
A nasa jawabin shugaba Tinubu ya buƙaci gwamnoni su mai da hankali wajen inganta walwalar ‘yan Najeriya ta hanyar zuba jari a muhimman ɓangarori na noman zamani da samar da wutar lantarki a yankunan karkara da yaƙi da talauci da bunƙasa ilimi.
“Ina son na roƙe ku da mu haɗu mu canja halin da mutane da ke yankin karkara. Tattalin arziƙi na bunƙasa. Muna kan samun bunƙasa tattalin arziƙi, amma muna da buƙatar kawo cigaba a yankunan karkara. Ya kamata mu haɗa kai wajen ciyar da al’umma gaba,” in ji shugaba Tinubu.
Shugaba Tinubu ya yi kira da a faɗaɗa shirin ciyarwa a makarantu da jan hankalin iyaye wajen kawo ‘ya’yansu makaranta da rage mawuyacin halin da yara ke fama da shi. Ya kuma ba wa majalisar zartarwa umarnin samar da kwamitin na musamman da zai riƙa bibiyar ayyukan cigaba da ake yi musamman na titin Lagos-Calabar da Sokoto-Badagry.
Dabarun kawo cigaba a matakin mazaɓu ya shafi ƙoƙarin tabbatar da kowa ya samu cigaba ta hanyar haɗin guiwa a tsakanin matakan gwamnatin uku da ake da su a Najeriya.