Gwamna Abba Ya Amince Da Gina Sabon Babban Masallaci Na Zamani A Unguwar Rijiyar Zaki – Kano
A yau Juma’a 1 ga Agusta, 2025, gwamnatin jihar Kano ta amince da gina sabon babban masallaci na zamani a unguwar Rijiyar Zaki, wanda zai kunshi dakin karatu, rijiyar ruwa, da cibiyar koyar da Al-Qur’ani.
Wannan aikin na cikin sabbin tsare-tsaren Gwamna Abba Kabir Yusuf na bunkasa al’umma da kyautata rayuwar addini da ilimi.
Al’umma sun bayyana farin cikinsu, inda wasu malamai suka ce hakan zai hana matasa yawo marar dalili tare da dawo da darajar masallatai a cikin gari.