A yau Laraba, Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da Dokar Canjin Yanayi tare da kafa kwamitin aiwatarwa mai suna Steering Committee. Wannan sabon shiri na da burin shuka itatuwa miliyan 5 a fadin jihar kafin ƙarshen shekara.
Kwamishinan muhalli ya bayyana cewa wannan tsari zai kuma hada da samar da makamashi mai tsafta, rage hayaƙin motoci, da ilimantar da jama’a game da illar dumamar yanayi.
Gwamnatin jihar ta lashi takobin canza rayuwar muhallin Kano daga sahara zuwa kore cikin shekaru kalilan.
Asrah 24 TV – Gaskiy
ar Zance
