Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani gagarumin shirin dakile cutar Malaria a karamar hukumar Madobi. Wannan yunkuri ya haɗa da rabon labule masu kashe kwari (ITNs) da kuma magungunan kariya ga yara da mata masu juna biyu.
Rahotanni sun nuna cewa an ware sama da naira miliyan 140 don wannan aiki, tare da raba kayayyakin haihuwa fiye da 6,000 da kuma kayan C‑Section guda 500 a asibitocin jihar.
Wannan yunkuri na daga cikin matakan Gwamna Abba Kabir Yusuf na kare rayukan mata da ƙananan yara a jihar, inda ya bayyana cewa
Ba za mu ƙara yarda mace mai juna biyu ta mutu a Kano saboda rashin kulawa ba.”
Asrah 24 TV – Gaskiyar Zance
