Wani matashi mai shekaru 30 an gurfanar da shi a gaban kotun shari’ar musulunci da ke Kano bisa zargin satar wayar Infinix Hot 11 mai kimanin ₦91,000.
Lauyan gwamnati ya ce wanda ake zargi ya kutsa cikin wani shago ya yi amfani da ruwa mai ƙarfi wajen cire wayar daga inda ake ajiyeta. Duk da haka, ya musanta laifin a gaban kotu.
Alkalin ya dage sauraron shari’ar zuwa mako mai zuwa domin ci gaba da bincike da karar daga bangarorin biyu.
Asrah 24 TV – Gaskiyar Zance
