Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya samu yabo daga wata ƙungiya ta masu ruwa da tsaki (Forum) bisa yadda aka gudanar da aikin Hajj 2025 cikin tsari, mutunci da kulawa ga alhazai.
Ƙungiyar ta bayyana cewa gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa almajirai daga jihar sun samu kulawa ta musamman, musamman ma marasa ƙarfi, ta yadda suka iya aiwatar da ibadarsu cikin walwala da sauƙi.
A cewar rahoton, hadin kan shugabanci da tsari mai kyau da aka nuna a wannan hajj, ya zamo abin koyi, inda mutane da dama suka bayyana cewa “an rubuta sabon tarihi a Kano” a fannin gudanar da aikin hajji.
✈️ An Karɓi Gwamna da Dumi-dumin Tarba
Bayan dawowarsa daga kasar Saudiyya, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu tarba mai zafi daga jama’a, wanda ke nuna irin ƙaunar da suke masa da kuma gamsuwa da yadda ya tsaya tsayin daka wajen ganin an yi aikin hajji cikin kwanciyar hankali.
Wannan nasara ta sake bayyana irin hangen nesa da kishin addini da al’umma da gwamna ke da shi.
