A wani zama da aka gudanar a Kaduna don bitar tsarin mulkin Najeriya, Mataimakin Gwamna, Aminu Gwarzo, ya gabatar da bukatar Kano:
Ƙirƙirar sabuwar jiha guda ɗaya a yankin Kano
Ƙara kananan hukumomi 26 a cikin jihar
An bayyana cewa wannan mataki zai kusantar da gwamnati zuwa ga jama’a, ƙarfafa ci gaban yankuna da samar da ayyuka da dama.
Wannan shiri na ƙara LGAs da jiha sabuwa zai canza fasalin siyasa da tattalin arziki a Arewacin Najeriya baki ɗaya.
