Mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ja kunnen masu sukar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa kada su raina kokarin da shugaban ke yi wajen sauya Najeriya.
A yayin wani taro kan tsaron intanet da aka gudanar a ranar Talata a birnin Abuja, Ribadu ya bayyana cewa Najeriya a karkashin mulkin Tinubu na kara samun tsaro, kwanciyar hankali da kuma janyo hankalin masu zuba jari, sakamakon wasu muhimman gyare-gyare da gwamnatin ke aiwatarwa.
Ya kuma siffanta masu suka da tsoffin ‘yan siyasa da suka ƙare tasirinsu, amma ke ci gaba da neman dora ra’ayoyinsu ga kasa koda kuwa ba su da sabon tunani ko sahihin gudummawa ga ci gaban ƙasa.
“Wasu na jin kamar ba za a iya tafiyar da kasa ba sai su, alhali lokacin su ya wuce. Wannan gwamnati na kokari kuma tana da jajircewa wajen gyara Najeriya,” in ji Ribadu.
Sai dai kalaman Ribadu na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma da dama ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, ciki har da yawaitar garkuwa da mutane a jihohin Arewa da kuma hare-haren Boko Haram da har yanzu ke ci gaba da faruwa a sassa daban-daban na kasar, lamarin da ke haifar da tambaya kan ikirarin samun nasarorin tsaro da ya yi.
A halin yanzu, yawancin ‘yan Najeriya – musamman ma a yankin Arewa – na ci gaba da kokawa kan rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki, duk da irin fatan alheri da gwamnatin Tinubu ta nuna a farkon mulkinsa.
