Dr. Kassim Ya Dace da Kujerar!” — Daraktan UBEC Ya Yabi Gwamna Sule
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya samu yabo daga Daraktan Yankin Arewa ta Tsakiya na Hukumar Ilimin Firamare ta Ƙasa (UBEC), Elder Edward Abalaka, saboda nadin da ya yi wa Dr. Kassim Muhammad Kassim a matsayin Shugaban Hukumar NSUBEB ta jihar.
Yayin wata ziyara ta taya murna da ya kai tare da wasu jami’an UBEC, Abalaka ya bayyana cewa Dr. Kassim ya dace da kujerar, yana mai cewa:
“Wannan nadin dai kamar square peg in a square hole ne – mutum ya dace da aikin da aka dora masa.”
Ya ci gaba da yabawa Dr. Kassim da cewa yana gwagwarmaya don inganta ilimin firamare a Jihar Nasarawa.
Elder Abalaka ya bayyana cewa tun cikin kankanin lokaci da Dr. Kassim ya hau kujerar shugabanci, ya aiwatar da muhimman sauye-sauye, ciki har da:
Warware ayyuka marasa inganci da aka riga aka biya su;
Biya da kansa albashin masu tsabtace makarantar Smart na watanni 5 da aka basu bashi;
Matsar da wani shugaban makaranta saboda rashin tsayawa aikin sa yadda ya kamata;
Da kuma saya wa ƙungiyar yaɗa labarai motar aiki.
A nasa bangaren, Dr. Kassim Muhammad Kassim ya nuna godiya ga tawagar ta UBEC saboda yadda suka ba shi lokaci suka kai masa ziyara, inda ya ce:
> “Dukkan abin da muke aiwatarwa, bin manufofin ilimi ne na Gwamna Abdullahi Sule.”
