Sokoto Kaduna Zamfara Na Daga Cikin Jihohi 20 Da Ke Fuskantar Barazanar Ambaliya Duk Da N620bn Da Aka Ware
Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NiMet) ta fitar da gargaɗi game da yiwuwar ambaliya a watan Yuli, tana mai cewa jihohi irin su Sokoto, Lagos, Edo, Benue, da wasu jihohi 16 na cikin haɗarin ambaliya sakamakon ƙaruwar samun ruwan sama.
Wannan ya zo ne yayin da ƙungiyoyin Africa Environmental Health Organisation, masana sauyin yanayi, da Nigerian Institute of Town Planners suka soki gwamnatocin jihohi saboda gazawa wajen magance ambaliyar da ta ɓarke a sassa da dama na ƙasar, duk da cewa an raba sama da naira biliyan 620 a matsayin kudaden kula da muhalli (Ecological Funds).
Cikin sanarwar da NiMet ta fitar a ranar Litinin 07 ga Yuli 2025, ta bayyana cewa akwai yiwuwar ambaliya a jihohi kamar haka: Sokoto, Kaduna, Zamfara, Yobe, Bauchi, Bayelsa, Jigawa, Adamawa, Taraba, Niger, Nasarawa, Benue, Ogun, Ondo, Lagos, Delta, Edo, Cross River, Rivers, Akwa Ibom.
A karshe hukumar ta shawarci mazauna wadannan yankuna su kasance cikin shiri, tare da tsaftace magudanan ruwar su.
