IMF Ta Gargaɗi Najeriya Kan Bukatar Sauya Kasafin Kuɗi Saboda Raguwar Farashin Mai
IMF ta ce Najeriya na buƙatar yin gyaran kasafin kuɗi don daidaita da farashin mai a duniya da ya faɗi zuwa $68/barel, ƙasa da ƙimar da aka tsara ($75/barel).
Duk da samun ci gaba 3.4 % a bunƙasa tattalin arzikin Najeriya, IMF ta ce akwai buƙatar ƙarin matakan rage ƙimbin talauci da rashin abinci.
Sun shawarta gwamnati ta amfani da tsarin ƙarin tallafin kuɗi kai tsaye (cash transfer), kuma a ƙarfafa manufofin kuɗi don dakile hauhawar farashin kaya.
