A yau, ƙasashen Turai da dama sun shiga cikin wani matsanancin zafi da ake kira heat dome, wato iska mai zafi da ke kulle sararin sama.
Spain: 45.8°C
Faransa: 41.3°C
Birtaniya: Sama da 33°C
Hukumomi na ƙasashen Spain, Faransa, da Portugal sun fitar da gargadi kan haɗarin gobara da matsalolin lafiya da ke iya biyo baya.
Masana sun bayyana cewa wannan matsala tana da alaƙa kai tsaye da canjin yanayi (climate change) kuma hakan na nuna yadda yanayin duniya ke ƙara rikicewa da wuri fiye da da.
🔹 An shawarci mutane su guji fita da rana sosai, su sha ruwa da yawa, su kuma kula da tsofaffi da yara.
🟦 Asrah 24 TV –
Gaskiyar Zance.
