Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci wata babbar tawaga zuwa birnin Madina a ƙasar Saudi Arabia domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Dantata, ɗaya daga cikin manyan attajirai kuma jigo a harkar kasuwanci a Najeriya.
Tawagar ta haɗa da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da wasu manyan jami’an gwamnati da ‘yan uwan marigayin. Alhaji Aminu Dantata ya rasu a Abu Dhabi a ranar Asabar da ta gabata.
Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin “gwarzo mai taimakon al’umma da ƙasarsa da gaskiya.
🟦 Asrah 24 TV – Gaskiyar zance
