Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta tuntubi masu hannu da shuni a nan Kano dama Najeriya baki daya dan ganin an tallafawa yan kasuwar waya ta Farm Center da suka gamu da Iftila’in Gobara.
Kwamishinan ayyuka na musamman kuma shugaban kwamatin da gwamnati ta kafa dan Duba irin Asarar da gobarar ta yi Alhaji Nasir Sule Garo ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara ta musamman da kwamatin ya kai kasuwar.
Nasir Sule Garo ya kuma ce kwamatin zai amfani da Asusu guda daya ne dan Tara kudaden da za a tallafawa yan kasuwar.
Da yake jawabin godiya Sakataren kungiyar yan kasuwar wayar ta Farm Center Kwamred Ishak Abdulfatahi godewa gwamnatin ta Kano ya yi bisa kokarin da take na ganin an tallafawa yan kasuwar.
Yayin ziyarar kwamatin ya zaga cikin kasuwar dan ganin irin asarar da gobarar ta haifar.
