Gwamnatin jihar Kano ta haramta gabatar da al’adar nan da wasu ke gudanarwa a lokacin bukukuwa da ake kira da Kauyawa Day.
Shugaban hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jihar Kano Alhaji Abba Almustafa ne ya sanar da hakan.
Ya kuma ce sun dauki matakin ne biyo bayan korafe korafen da Jama’a suka kai mata ciki harda limamai da dattawa da kuma kungiyoyi kan abubuwan da ake gudanarwa a gurin bikin na Kauyawa na rashin tarbiyya.
Alhaji Abba Almustafa ya kuma ce daga yanzu hukumar ta kuma dakatar da lasisin duk wani gidan biki a fadin jihar biyo bayan sabunta dokokin hukumar da akai, inda yace dole sai duk wani mai gidan biki na Even center ya zo ya sabunta lasisinsa.
Ya kuma ce za su hada kai da Jami’an tsaro iri daban daban ciki harda hukumar Hisba data bijilantee dan ganin matakain da suka dauka suntafi yadda ya kamata.
