Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta biyawa daliban da suka samu narar cin darusa biyar a jarrabawar Qualifying da sukai kudin jarrabawar NECO ko NBAYIS ko kuma NAPTIC.
Kwamishinan ma’aikatar Ilimi Dakta Ali Haruna Makoda ne ya bayyana hakan a zantawarsa da jaridar Asrah 24tv.
Ya kuma ce gwammatin ta Kano za ta biya kudin jarrabawar NECO ko NBAYIS ko kuma NAPTIC ne ga daliban.
Kazalika ya ce gwamnatin ta Kano za ta kashe sama da naira Tiriliyan uku wajen biya. kudaden.
