Kungiyar daliban Kwalejojin kimiyya da fasaha na Polytechnic dake kasar nan sun baiwa hukumar dake lura da bayar da Laminin Ilimi ta kasa wa’adin kwanaki biyar kan ta yi cikakken bayanin yadda aka kashe kudaden daliban.
Shirin ba da lamunin ya bayyana hakan ne biyo bayan zargin da hukumar wayar da kan jama’a ta kasa ta yi na cewa wasu cibiyoyi tare da hadin gwiwar bankuna na ci gaba da cire kudaden rancen dalibai na bogi.
Wadannan zarge-zarge dai sun janyo ce-ce-ku-ce, inda har ya kai ga wata zanga-zangar da ‘yan kungiyar dalibai ta kasa suka gudanar a ranar Litinin da ta gabata, inda suka tare hanyar Legas zuwa Ibadan.
