Hukumar tace Fina-finan da Dab’i ta jihar Kano ta ce yanzu haka tanakan bincike don gano yadda akai mawaki Hamisu Breaker ya saki sabuwar wakarsa mai suna Amanata ba tare da an tantanceta ba.
Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radio.
Ya kuma ce aikin dakatar da wakar ba na hukumar Hisbah bane na hukumar tace fina-finai ne amma ba laifi bane dan hukumar ta Hisbah ta magantu akai domin dama suna aiki kafada da kafada ne.
Mai magana da yawun hukumar ta ce fina-finai da Dab’i ta jihar Kano Abdullahi Sani Sulaiman kenan.
