Ana fargabar tashin farashin man fetur a Najeriya biyo bayan matakin da kamfanin NNPCL ya dauka na dakatar da siyar da danyen mai ga matatun cikin gida, ciki har da ta Dangote, da takardar Naira.
Rahotanni daga jaridar The Cable sun bayyana cewa yanzu NNPCL zai rika sayar da danyen mai ne kawai da Dala, wanda hakan na iya haifar da karin farashi, musamman ganin yadda matatun mai a Najeriya za su fara neman Dala daga kasashen waje.
Tun a shekarar 2024, Shugaba Bola Tinubu ya umarci NNPCL da ta siyar da danyen mai da Naira don kara darajar kudin kasar da saukaka aiki ga matatun cikin gida. Sai dai, duk da an tsara cewa shirin zai dore har zuwa 2030, wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa an dakatar da shi tun yanzu, lamarin da ka iya haddasa hauhawar farashin fetur a kasuwannin cikin gida.
