Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC tare da komawa SDP.
Rahotanni daga Vanguard sun bayyana cewa El-Rufai ya wallafa sanarwar a shafinsa na Facebook a yau Litinin, inda ya ce tuni ya mika takardar ficewarsa ga shugabancin jam’iyyar a mazabarsa bayan tattaunawa da magoya bayansa.
Ya zargi shugabannin APC da yin watsi da matsalolin cikin gida da tauye dimokuradiyya. A matsayinsa na mamba a SDP, El-Rufai ya sha alwashin jagorantar hadin kan jam’iyyun adawa domin kalubalantar APC a zaben 2027, yana mai cewa jam’iyyar ta riga ta dauke shi a matsayin mara muhimmanci, duk da cewa yana daga cikin masu kafa ta.
