Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta fara bincike kan mutuwar Hajara Isa, wata mata mai shekaru 20 da aka tsinci gawarta a gidan mijinta a ranar 28 ga Fabrairu, 2025.
Rahoton da aka kai wa ‘yan sanda a ranar 3 ga Maris ya nuna cewa iyalan mamaciyar na zargin kishiyarta, Fatima Mohammed, mai shekaru 28, da hannu a mutuwar ta.
Binciken farko ya kai ga cafke Fatima, wadda ta amsa cewa ita ce ta shake Hajara har lahira, sannan ta yi kokarin ɓoye laifin ta hanyar zuba mata ruwan zafi da kona gawarta da buhun robobi.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi, inda aka tura tawaga daga C Divisional Police Headquarters, karkashin jagorancin DPO. Ana ci gaba da bincike a sashen SCID, kuma ‘yan sanda sun bayyana cewa za a yi amfani da fasahohin zamani da kuma tono gawar mamaciyar idan bukatar hakan ta taso.
