Gwamnatin Kano ta bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya ba Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15, umarnin barin jihar domin kaucewa rikici a masarautar Kano.
Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana cewa kamata ya yi a mayar da Bayero Lagos tare da naɗa shi sarauta a can, maimakon a ci gaba da ba shi kariya a gidan Sarki na Nassarawa.
Wannan kiran na zuwa ne a matsayin martani kan matakin jami’an tsaro na ci gaba da kare Bayero a Kano, lamarin da gwamnatin ke ganin zai iya janyo matsala ga zaman lafiya a jihar.
