Wasu ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai farmaki a kauyen Kaleri da ke karamar hukumar Jere, kusa da jami’ar Maiduguri, inda suka sace mutane biyu tare da kwashe kayan abinci masu yawa.
Wata majiya ta tabbatar da cewa mayakan sun shiga kauyen dauke da manyan makamai, suna bi gida-gida domin karbar kayan abinci, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici.
Bayan harin, jami’an tsaro sun rufe hanyar da ta kusa da wurin, sannan suka kama wasu mutane biyu, ko da yake ba a tabbatar da alakar su da ‘yan ta’addan ba.
