Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta ƙasa (JAMB) ta bayyana cewa za ta rufe rijistar jarrabawar shekarar 2025 a ranar 8 ga watan Maris.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Talata, JAMB ta jaddada cewa ba za a ƙara wa’adin yin rijista ba, don haka masu niyyar rubuta jarrabawar su hanzarta kafin lokaci ya ƙure.
Tun daga ranar 3 ga watan Fabrairu aka fara rijistar, kuma zuwa yanzu, fiye da miliyan 1 da rabi sun kammala rajista, a cewar kakakin hukumar, Fabian Benjamin.
