Hukumar Dakile Yaduwar Cutuka ta Kasa (NCDC) ta bayyana cewa cutar zazzabin Lassa ta kashe akalla mutane 80 a Najeriya tsakanin 3 zuwa 9 ga watan Fabrairu, 2025.
A cewar NCDC, an samu raguwar yawan masu kamuwa da cutar idan aka kwatanta da baya. Sabbin rahotanni sun nuna cewa jihohin da aka fi samu masu fama da cutar sun haɗa da Bauchi, Ondo, Taraba, Edo, Gombe, Kogi, da Ebonyi.
