Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta hana ‘yan Najeriya da ke amfani da fasfo na ECOWAS shiga kasar, biyo bayan sabbin dokokin tafiye-tafiye da ta kafa.
Wannan matakin na zuwa ne bayan ficewar Nijar daga ECOWAS tare da kasashen Mali da Burkina Faso. Duk da cewa kasar bata rufe iyakokinta da Najeriya ba, amma ta dauki tsauraran matakai musamman a iyakokin Illela da Konni.
Matafiya da ‘yan kasuwa daga kasashen biyu sun fara fuskantar matsaloli sakamakon wannan sabuwar dokar da ke kara dagula alakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Nijar.
