Kazamin rikici ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da PDP a jihar Osun, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 8 a jiya Litinin. Rikicin ya samo asali ne sakamakon takaddama kan shugabancin kananun hukumomin jihar, duk da cewa kotu ta hana rushe shugabannin da ke rike da mukamai.
An ce an yi amfani da bindigu a rikicin, inda PDP ta ce an kashe magoya bayanta 5, yayin da APC ta ce an kashe mata mutane 3. Bayan faruwar lamarin, gwamna Ademola Adeleke ya umarci jami’an tsaro su shawo kan rikicin, yayin da ‘yan sanda suka ce za su yi karin bayani bayan bincike.
