Babbar kotun jihar Kano ta umarci Baban bankin kasa na CBN da kuma Hukumar rabon tattalin arzikin kasa kan su baiwa majalisun kananan hukumomin jihar Kano 44 kudinsu na wata wata bisa tanadin Doka.
A hukuncin da Mai sharia justice Ibrahim Musa Karaye ya karanta ya bayyana cewa masu Kara da suka hadar da kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin jihar Kano 44 da kungiyar Shuwagabannin kananan hukumomin jihar Kano 44.
Sun dai gabatarwa da kotun gamsassun bayanan da su ke tabbatar da cewa ya kamata a rinka biyansu kudaden su wata wata da ga asusun raabon tattalin arzikin kasa.
