Rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara ta kama wani malamin addini, AbdulRahman Bello, bisa zargin kashe wata daliba, Lawal Hafsoh Yetunde, domin yin tsafi da ita.
Marigayiyar, daliba ce a shekarar ƙarshe a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara, Ilọrin. An ce ta bace tun ranar 10 ga Fabrairu, 2025, bayan halartar wani bikin suna, inda ake zargin malamin ya kirawo ta a waya yayin da take cin abinci.
Rahotanni sun nuna cewa mamaciyar ta hadu da wanda ake zargi a dandalin sada zumunta na Facebook. Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama shi ta bakin kakakinta, SP Adeoun Ejire.
