Majalisar dokokin ƙasa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na ƙarin kasafin kuɗin 2025, wanda yanzu zai tsaya a Naira triliyan 54.9.
Tun da farko, majalisar ta amince da kasafin Naira triliyan 49.7, amma daga bisani Shugaba Tinubu ya nemi ƙarin zuwa Naira triliyan 54.2, bisa hujjar cewa gwamnati ta gano sabbin hanyoyin samun kuɗaɗe.
Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar dattawa, Olamilekan Adeola, tare da takwaransa na majalisar wakilai, Abubakar Bichi, ne suka gabatar da rahoton amincewa da sabon kasafin, wanda ya kai Naira triliyan 54.9.
