Shugaban Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Kasa (SSS), Oluwatosin Ajayi, ya bayyana cewa akwai buƙatar ba wa wasu daga cikin ‘yan Najeriya damar mallakar makamai domin kare kansu daga hare-haren ‘yan ta’adda.
Ajayi ya bayyana hakan yau yayin taron shekara-shekara na ƙungiyar AANISS da aka gudanar a Abuja, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci da matsalar tsaro.
Ya bayar da misali da garin Azare, Jihar Bauchi, inda mutanen gari suka haɗa kai suka fatattaki Boko Haram. Ya kuma jaddada cewa ba zai yiwu a ce sojoji da ‘yan sanda ne kaɗai za su iya bai wa kowane ɗan kasa cikakken tsaro ba.
