Kwamitin majalisar dattawa mai kula da asusun kuɗin ƙasa ya yi wa Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, tambayoyi kan bacewar bindigogi 178,459 daga rundunar ‘yan sanda da kuma zargin wata kwangilar Naira biliyan 1.1.
Rahoton babban mai binciken kuɗi na ƙasa a shekarar 2019 ya bayyana cewa mafi yawan makaman da suka bace sun haɗa da AK-47, wanda hakan ke ƙara tabarbarewar tsaro a ƙasar.
A lokacin da Egbetokun ya gaza bayyana a gaban majalisa, mataimakinsa AIG Abdul Sulaiman ne ya wakilce shi, yana mai cewa wasu daga cikin bindigun sun ɓace ne sakamakon hare-hare da fashi da makami.
Majalisar ta nuna damuwa cewa waɗannan makamai na iya faɗawa hannun bata gari, wanda ke ƙara ruruta matsalar tsaro a Najeriya.
