Ɗaya daga cikin mambobin majalisar wakilai na jam’iyyar PDP, Salisu Garba Koko, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa APC.
Garba Koko, wanda ke wakiltar mazabun Besse/Maiyama Yema a Jihar Kebbi, ya bayyana cewa rikicin cikin gida da ya mamaye PDP kuma aka gaza shawo kansa ne ya sa ya yanke shawarar sauya sheka.
Kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas, ne ya karanto wasikar ficewar Koko yayin zaman majalisar na yau Laraba.
Sai dai, shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda, ya musanta cewa PDP na fama da rikicin da zai sa wani ya fice daga jam’iyyar.
