Wasu masana harkokin crypto a Arewa sun bayyana cewa babbar kasuwar crypto ta OKX zata fara cinikayyar Pi Network a ranar 20 ga Fabrairu, 2025. Wannan na zuwa ne bayan da Pi Network suka tabbatar da fara Open Mainnet a wannan rana, wanda ke nufin an kusa kawo karshen dogon jiran da masu mining suka yi tun daga 2019.
Masana dai na hasashen cewa Pi Network na iya samar da babbar riba ga masu mining, sai dai wasu na ganin kudinsa zai karu ne bayan ya jima a kasuwa. Wannan ci gaba na iya zama wata babbar dama ga ‘yan crypto a Najeriya da ma duniya baki daya.
