Hukumar NDLEA reshen Kano ta ja hankalin iyaye su kula da tarbiyyar ‘ya’yansu, bayan kama matasa 80—mata 30 da maza 50—da ake zargi da shan kayan maye yayin bikin zagayowar ranar haihuwa. Kakakin hukumar, Sadik Muhammad Maigatari, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce an kama matasan tun a watan da ya gabata. Hukumar ta yi kira ga iyaye da su saka ido kan halayen ‘ya’yansu domin kaucewa fadawa cikin matsalar shaye-shaye.
NDLEA Kano Ta Gargadi Iyaye Bayan Kama Matasa 80 Masu Shan Kayan Maye a Bikin Birthday,
Previous ArticleDan Bijilanti Ya Kashe Budurwarsa Saboda Taki Zubar da Ciki
Related Posts
Add A Comment
