Dan majalisa mai wakiltar Jaba da Zangon Kataf, Amos Gwamna Magaji, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da komawa APC. Ya bayyana cewa rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP ne ya tilasta masa sauya sheka. Ya kuma yi alkawarin bayar da gudunmawa ga APC a mazabunsa.
Sai dai shugaban marasa rinjaye na majalisa, Kingsley Chinda, ya kalubalanci matakin, yana mai cewa Amos bai bi ka’ida ba. Ya bukaci kakakin majalisa da ya ayyana kujerarsa a matsayin wadda aka kwace, domin gudanar da sabon zabe a mazabun.
