Majalisar dokokin Kano ta yi dokar kafa hukumar kula da ƙanana da matsakaitan masana’antu a jihar domin inganta ƙananan masana’antu wanda hakan zai samarwa da al’ummar jihar ta Kano domin rage zaman banza ga matasa a faɗin jihar.
Da yake ƙarin haske ga manema labarai shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala yace wannan kafa hukumar da akayi gwamnatin Kano zata samar da duk wasu tsare-tsare da zasu inganta masana’antun wajen basu duk wasu kayan aiki da zasu ciyar da masana’antun gaba.
A wani labarin kuma Majalisar dokokin ta yi kira ga dokar amfani da ƙasa wato Land Use domin gyara akan ta, ta yadda al’umma zasu mallaki ƙasa tare da sabunta takardun su batare da samin matsala ba kasancewar yadda ake samun matsala akan hada hadar ƙasa a faɗin jihar.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ne ya gabatar da ƙudirin gaggawa a zaman majalisar na yau.
Dokar ta tanadi yadda za’a rarraba mallaka da amfani da ƙasa, haka kuma dokar ta bada ikon mallakar duk wata ƙasa ga gwamnatin tarayya da jihohi, tare da baiwa gwamnoni ikon bayar da izini ga mutanen da za su yi amfani da ita.
