Gwamnan Zamfara, Dr. Dauda Lawan Dare, ya bayyana cewa zai yi sulhu da ‘yan bindiga ne kawai idan sun ajiye makamai tare da mika wuya. Yayin zantawa da BBC, ya ce a baya ya ki amincewa da sulhu saboda barnar da suka tafka da kuma yadda ake ba su kudi a lokutan baya. Gwamnan ya jaddada cewa suna samun nasara a yaki da ‘yan ta’adda, inda fiye da 50 aka kashe a Tingar Fulani. Sai dai a yanzu, ya ce sulhu abu ne mai kyau idan an yi shi ta hanya madaidaiciya.
Previous ArticleJami’ar ATBU ta bawa Dalibai Damar Amfani da Gas domin yin girki
Related Posts
Add A Comment
