Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, inda suka yi ganawar sirri a dakin karatu na OOPL dake Abeokuta, jihar Ogun. Atiku ya samu rakiyar tsohon gwamnan Cross River, Liyel Imoke, Aminu Tambuwal, da Sanata Abdul Ningi. Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin ziyarar ba, ana hasashen tana da alaka da siyasar Najeriya, musamman ganin zaben 2027 na karatowa.
