’Yan bindigar da suka sace tsohon shugaban hukumar NYSC, Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), sun nemi a biya Naira miliyan 250 kafin su sako shi.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace Tsiga tare da wasu mutane 9 a daren ranar Laraba a kauyen Tsiga, karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina, yayin da suke tsaka da bacci.
Wata majiya daga iyalansa ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa masu garkuwar sun tuntube su dangane da bukatar biyan kudin fansa. Kawo yanzu, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba ta ce komai ba kan batun.
