Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban hukumar NYSC, Manjo Janar Mahraz Tsiga, tare da wasu mazauna kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa an sace su ne a tsakar daren Laraba, duk da cewa har yanzu hukumomi ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba. Wata majiya ta shaidawa Prime Time cewa tabbas tsohon shugaban NYSC yana cikin wadanda aka sace.
Zuwa yanzu, ba a samu karin bayani daga gwamnatin jihar Katsina ko rundunar ‘yan sanda game da wannan sace-sace ba.
