A yayin da wa’adin rufe karɓar kuɗin aikin hajji ke ƙaratowa, mahukuntan Ghana sun sanar da rage kuɗin aikin hajji daga Cedi 75,000 zuwa Cedi 62,000, wanda ya yi daidai da Naira 6,608,000. Wannan matakin ya zo ne bisa alkawarin da Shugaba John Mahama ya ɗauka na sauƙaƙa wa Musulmai wajen biyan kuɗin hajji.
A gefe guda, ‘yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan tsadar kuɗin aikin hajji, wanda ya zarce Naira miliyan 8, kamar yadda hukumar aikin hajji ta ƙasa ta bayyana kwanan nan.
