Tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa goyon bayan jam’iyyar APC ce mafita ga matsalolin da Najeriya ke fuskanta.
Masari ya bayyana haka a jiya Lahadi yayin kaddamar da yakin neman zaben kananan hukumomi a karamar hukumar Kafur, yana mai kalubalantar masu shirin kafa jam’iyyar hadaka don kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Ya ce rashin samun mukamai ne ke haddasa wannan yunkuri, amma duk da haka, APC za ta ci gaba da rike mulki. A cewarsa, a matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar, zai jajirce wajen tabbatar da manufofinta da ci gabanta.
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da cewa za a gudanar da zabukan kananan hukumomi a ranar 15 ga watan Fabrairu.
