Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kamfanin jiragen sama na Max Air na tsawon wata uku bayan fashewar tayar jirgin a daren Talata a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano , dake nan Kano.
Da yake sanar da dakatarwar a ranar Laraba 29 ga watan Janairun 2025 jami’in yada labaran hukumar lura da harkokin sufurin jirage ta kasa (NCAA) Micheal Achimugu, ya ce ana ci gaba da bincike kan abinda ya haifar da matsalar.
Achimugu ya ce ya yin dakatarwar ta wata uku hukumar ta NCAA, zata yi kwakwaran binciken tabbatar da lafiyar jiragen kamfanin Max Air.
Lamarin na baya baya nan shi ne karo na uku cikin watanni Uku da jiragen kamfanin na Max Air ke samun Matsala.
