Masana ilimin muhalli da zamantakewar dan Adan sun ce samar da tsaftataccen ruwa ga al’umma zai rage yawan cutuka da ake samu.
Dakta Musa Abdullahi Sufi masanin muhalli a nan Kano kuma malami a Jami’ar Maryam Abacha dake nan Kano ne ya bayyana hakan lokacin da gidauniyar tallafawa mabukata ta Widi Jallo ke kaddamar da rijiyar Burtsatse ta dari biyar da suka samar a fadin kasar nan harma da makwabtan kasashe a gidan adana namun daji na Zoo.
Dakta Musa Abdullahi Sufi ya kuma ce idan har ganyayyakin da dan adam ke ci suna samun tsaftataccen ruwa za a rage yawan cutukan da ake samu.
Ya kuma ce dukkan mahallin da ya wadata da ruwa maitsafta za a samu kowanne irin ci gaba da ake bukata a cikin sa.
Da yake jawabi yayin kaddamar da gina rijiyar Burtsatsen ta dari biyar a gidan adana namun daji na Zoo shugaban gidan Kwanzabeta Sadik Kura Muhammad cewa ya yi za su ci gaba da baiwa Gidauniyar ta Widi Jallo dukkan hadinkan da ake bukata.
Ita kuwa ana ta jawabin shugabar tsare-tsaren ayyukan gidauniyar Hajiya Bilkisu Hamisu Mai Iyali godewa alumma ta yi kan yadda suke basu hadin kai wajen gudanar da ayyukan su.
A nasa jawabin shugaban gidauniyar ta Widi Jallo Alhaji Abubakar Widi cewa ya yi za su ci gaba da tallafawa mabukata.
Gidauniyar ta Widi Jallo ta gina rijiyoyin Burtsate dan tallafawa mabukatan da basu da ruwa a jihohin kasar nan da wasu daga cikin kasashen makwabta.
